Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: A jawabinsa, ya bayyana Imam Khumaini a matsayin wata baiwa daga Allah, wanda ya ce ya canza tunanin al'umma tare da samar da sauye-sauye. "Imam ya kawo sauye-sauye, ciki har da Intizar. Ya sauya wa mutane fahimta a kan wannan. Intizar ba zama ne kawai ba, aiki ne kafin bayyanarsa (Imam Mahdi) da kuma bayan bayyanarsa." Ya kara da cewa, ya kuma sauya yadda duniya ke kallon addini, inda aka fahimci addini a matsayin hanyar samun ƴanci, ba hanyar danne mutane ba kamar yadda ake nunawa kafin zuwansa.
A ci gaban jawabinsa, ya ce Imam ya koyar da duniya cewa iko yana hannun mutane, kuma ta hanyar yaƙar zalunci da dogaro ga Allah ne ake samun nasara. "Maƙiya na tsoron tasirin fikirarsa a cikin al'umma, wanda ya sa suke ci gaba da yaƙi tare da ƙoƙarin dakile yaɗuwar wannan fikira." A ƙarshe, ya yi kira ga al'umma da su yi riƙo da fikirarsa, yana mai cewa, "Imam Khumaini yana nan, domin fikirarsa tana nan. Ba wata sabuwa za a yi ba; abin da ya rage wa mutane shi ne su bi ta. Ita ce fikirar da Shaheed Sayyid Khamenei ya tsaya ƙyam a kai. Duniya tana buƙatar komawa ga bin fikirarsa (Imam Khumaini), domin ita ce mafita gare ta."
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
16/DhulHijja/1447
02/06/2026
Your Comment